BANI HANKALINKA (Paper 2 )
Kun b'ata da wane dan'uwanka ayau, gobe ma kun b'ata da wane makocinka ko abokin aiki, shin baka tunanin cewa idan ka mutu sune masu kaika makwanci? Shin kokuwa kamanta su za'a tambaya halayyarka bayan bakanan ballantana kace karya suke? Kuma sudin dai ne zasu cigaba da bada tarihinka har abin yashafi zuriyarka.