Posts

Showing posts from November, 2022

BANI HANKALINKA (Paper 2 )

 Kun b'ata da wane dan'uwanka ayau, gobe ma kun b'ata da wane makocinka ko abokin aiki, shin baka tunanin cewa idan ka mutu sune masu kaika makwanci? Shin kokuwa kamanta su za'a tambaya halayyarka bayan bakanan ballantana kace karya suke? Kuma sudin dai ne zasu cigaba da bada tarihinka har abin yashafi zuriyarka.

BANI HANKALINKA

 Shin ko ka fahimci cewa akwai darussa masu yawa acikin yadda zakaga kowa yana gudu akan titi? Wani yana sauri ne domin ya riski arziki ko wata qaddara kamar yadda qudura ta tsara masa. Wani kuwa gudu yake domin cimma ajalinsa, amma cikinsu babu wanda yasan hak'ik'ar inda zaije.